On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Bullar Wasu Tsuntsaye Da Farin ‘Dango Dake Cinye Amfanin Gona A Jihohi 3 Na Najeriya.

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da mamayar tsuntsaye da Farin ‘Dango da ke lalata amfanin gona a jihohi uku na Arewacin kasarnan da suka hada da Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Babbar jami’ar kula da lafiyar dabbobi ta tarayya, Dakta Maimuna Habibu, ta ce an samu rahoton bullar wasu farin ‘Dango  musamman a jihohin Zamfara da Kebbi.

Dakta Maimuna ta ce bayan karbar korafe-korafen, tuni ma’aikatar ta tura jami’anta domin daukar matakai ta hanyar  Feshi ta  sama  a jihohin da abun ya shafa.