On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Gwamnatin Tarayya Ta Zargi Wasu Manyan Masu Fada Aji Da Daukar Nauyin Aiyukan Ta'adanci

Dele Alake

Ministan Ma’adinai, Dele Alake ya zargi wasu manyan masu fada aji a kasar nan da hannu dumu-dumu cikin aiyukan hakar ma’adinai ta barauniyar hanya, da kuma daukar nauyin aiyukan ‘yan bindiga da ta’adanci a kasar nan.

Ministan ya yi wadannan zarge-zarge ne a yayin da ya baiyana  gaban kwamitin  majalisar wakilai mai saka ido  kan harkokin Ma’adinai a ranar Talata, domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa.

Ya ce  irin wadannan  miyagun aiyuka  na mutanen na  temakawa wajen daukar  nauyin miyagun lefuka, a maimakon su bada gudunmuwarsu wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

 Ya  kara da cewar dole ne  sai gwamnati ta yaki matsalar domin samar da cigaban da ake  muradi.