Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na dasa bishiyoyi miliyan 20 a shekarar 2026 domin yaƙi da hamada, ambaliyar ruwa da kuma sauyin yanayi.
Haka kuma ta bayyana aniyarta ta ƙarfafa dokoki domin hukunta mutane da ƙungiyoyin da suka gaza kare muhalli.
Ministan Muhalli, Malam Balarabe Abbas Lawal, ne ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Great Green Wall ta shekarar 2026, ƙaddamar da kamfen ɗin dasa bishiyoyi na ƙasa da kuma rantsar da Kwamitin Jagoranci na Ƙasa na SURAGGWA, da aka gudanar a Kano.
Ministan ya ce shirin na da nufin samar da jerin bishiyoyi a yankunan da ke fuskantar barazanar hamada da sauran matsalolin muhalli. Ya kuma bayyana Kano a matsayin hedikwatar Hukuma mai rajin kare muhalli ta Ƙasa ta Great Green Wall (NAGGW).
Comments
Add a comment