Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin farfado da aikin Dam ɗin Kafin Zaki da aikin ban ruwa da aka daɗe da yin watsi da su a ƙaramar hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi, shekaru da dama bayan da aka fara tsara aikin tun zamanin Jamhuriyar Najeriya ta Biyu.
Manajan Daraktan Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are, Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, ne ya bayyana hakan yayin bikin Ranar Koguna ta Duniya ta shekarar 2026 a Ganjuwa.
Ya ce dam ɗin, wanda aka kiyasta yana da ƙarfin ɗaukar ruwa kimanin mita kubik miliyan 450, kuma aka tsara shi domin samar da ruwan ban ruwa ga kusan hekta 50,000 na gonaki, na da damar sauya fasalin noma da samar da amfanin gona a yankin.
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad, wanda Kwamishinan Filaye da Binciken Ƙasa, Abdullahi Muhammad Gwaram, ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar ta himmatu wajen kare kogunan jihar.
A nasa jawabin, hakimin Kariya da ke Ƙaramar Hukumar Ganjuwa ta Jihar Bauchi, Dauda Yakubu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta mayar da wasu sassan dazuzzukan da ke kewaye da al’ummominsa zuwa gonaki, domin rage wuraren da masu garkuwa da mutane da sauran miyagu za su iya fakewa.
Yakubu ya ce wasu al’ummomi suna da nisan ƙasa da kilomita ɗaya daga dajin, lamarin da ke jefa mazauna yankin cikin barazanar matsalar tsaro.
Ya kara da cewa babban dajin ya miƙe har zuwa Falgore a Jihar Kano da wasu sassan Jihohin Filato da Kaduna, abin da ke sa sa ido a kansa ya yi wahala tare da yiwuwar samar wa miyagu wuraren fakewa.
Shugaban gargajiyar ya ce mayar da wuraren da suka dace daga cikin dajin zuwa gonaki zai taimaka wajen inganta tsaro tare da samar wa mazauna yankin ƙarin filayen noma.
Comments
Add a comment