On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Gwamnatin Tarayya Zata Karya Farashin Dala

Shugaban kwamitin sauya fasalin hanyoyin tattara haraji na kasa, Taiwo Oyedele ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar sabbin tsare-tsaren da gwamnati ta bullo da su kan batun canjin kudin kasashen waje, za su temaka wajen inganta darajar Naira.

Ya  ce tsare-tsaren  wanda  suka hada  da  yaki  da duk wani haramtaccen tsarin musayar  kudi  zai  sa  darajar  naira  ta  cike  gibin da aka yi mata kafin shiga  sabuwar  shekarar   2024.

A  yayin ganawarsa  da manema Labarai a jiya, Mister  Oyedele,  ya  ce  gwamnati  zata  bullo da wasu dokoki a faiyace  domin gudanar da  canjin kudi a bisa  farashi na hukuma,  bayan an samar da adadin dalar da ake bukata  har kimanin Dala bilyan 6 da milyan 700.