On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Tarayya Zata Karya Farashin Makamashin Gas

Masu siyen Gas

Gwamnatin tarayya ta bullo da wani tsari na inganta samar da Mamakashin iskar gas a fadin kasar nan, a wani mataki na magance matsalolin da suka shafi samar da makamashin da ake amfani das hi wajen yin girki.

Gwamnatin tarayya  ta kafa wani kwamiti  wanda aka dorawa alhakin bada shawarwari  kan yadda  za’a inganta samar da makamashin iskar gas din,  da  kuma karya  farashinsa a cikin kasa da mako daya.

Bayanin hakan na kunshe  ne cikin wata sanarwa  da kakakin  karamin ministan Man fetir  na kasa,  Ekperikpe  Ekpo  ya fitar.

Sanarwar  ta Ambato  karamin ministan Mai  na baiyana  daukar  wadan nan matakai  biyo  bayan tashin farashin makamashin Gas zuwa sama da naira  1 da 100  a wasu  sassa na kasar nan, daga naira  700  da ake  siyar dashi  kan kowane  Kilogiram daya.