On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnatin Tinubu Ta Gaji Bashin Trilliyan 1.5 Daga Gwamnatin Buhari - Minista

Ministan ayyuka, Sanata David Umahi ya ce ma'aikatarsa ta gaji bashin Naira trilliyan 1.5 daga tsohuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

A cewarsa, an kafa kwamitoci shida domin duba bashin Naira trilliyan 1.5 da ‘yan kwangila ke bin gwamnatin tarayya.

A cikin wata sanarwa a karshen mako, Umahi ya ce kwamitocin guda shida, daya a kowace shiyya za su duba takaddun shaidar bin bashin da aka samar kafin ranar 29 ga Mayu na  2023 da kuma daga ranar 29 ga Mayu 2023 zuwa yau.

Sanarwar mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa, Orji Uchenna Orji, ta bayyana cewa kwamitocin za su kuma yi nazari kan bambancin farashin da aka amince da su da kuma bada shawarwari ga mahukuntan ma’aikatar.