On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Gwamnoni Ne Ke Haddasa Rikicin Zabe, Inji Adams Oshiomhole

ADAMS OSHIMOLE

Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole, Ya dora alhakin tada rikicin zabe da aka fuskantar a lokutan zabe na baya akan gwamnoni, inda yace sun taka muhimmiyar rawa wajen tashin zauni tsaye, ta hanyar daukar nauyin ‘yan dabar siyasa.

Oshiomhole ya baiyana haka ne a Abuja, yayin wani taro da aka shirya mai taken, Abunda zai inganta yin zabe a Najeriya, inda ya bukaci  shugabannin siyasa  dasu marawa yunkurin   jami’an tsaro na ganin anyi zaben shekara ta  2023 cikin salama batare da samun tada jijiyar wuya ba.

Jigon jam’iyyar  APCn a matakin, ya kuma yi kira da a samu hadin kai tsakanin hukumar zabe ta kasa da shugabannin siyasa da kuma hukumomin tsaro.

Tsohon gwamnan jihar Edon, Ya godewa  shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kokarinsa na magance kalubalen tsaro  da  ya addabi kasar nan.