On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Gwamnonin Najeriya Zasu Gana Da Gwamnan CBN Kan Takaita Cire Kudi Da Sabbin Takardun Naira

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 za su gana da gwamnan babban bankin kasar CBN, Godwin Emefiele, kan sabon tsarin Takaita  cire kudade da kuma sake fasalin takardun kudin na naira.

 

Kakakin kungiyar gwamnonin Najeriya, Abdulrazaq Bello-Barkindo shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Yace taron zai gudana ne da karfe tara na dare.

Bello-Barkindo yace taron, bisa ga gayyatar da Shugaban gwamnonin,  Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sakkwato ya yiwa Emiefele, zai fara ne da karfe 9 na dare.

Da yake bayar da goron gayyatar, Darakta Janar na kungiyar gwamnonin Najeriya, Asishana Bayo Okauru, yace jaddawalin taro ya shafi manufofin CBN na sake fasalin kudin Naira.

More from Labarai