On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Har Yanzu Akwai Maniyyata Aikin Hajji Sama Da Dubu 5 Da Ba'a Kwashe Ba

Mahajatan Najeriya A layi

Duk da Karin lokacin da Hukumomin Saudiyya suka bawa Najeriya domin kwashe alhazanta, Har yanzu akwai Mahajatta sama da Dubu 8 dake tsammanin warabukka, A yayin da ya rage sa’oi 24 a rufe filayen tashi da saukar jiragen sama na kasar saudiyya

 

A jiya ne hukumar aikin hajji ta kasa ta fitar da wata sanarwa wadda  ta farantawa maniyyata aikin hajjin, game da Karin wa’adin kwanaki biyu da saudiyya ta bawa najeriya domin kwashe mahajjatan.

Kawo safiyar  litinin, an kwashe maniyatta aikin hajjin bana dubu 27 da 359 daga cikin dubu 33 da 971, yayin da har yanzu akwai ragowar  mahajatta dubu 5 da 641 da ba’a kaiga daukewa ba.