On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Har Yanzu Gwamnatin Kano Bata Siyawa Al'ummar Bagwai Jirgin Ruwa Ba [Jigon Rahotonmu Na Mako]

Shekara 'Daya bayan wani hatsarin kwale-kwale da ya afku a karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano, har yanzu al’ummar yankin na ci gaba da kokawa kan rashin cika alkawarin da gwamnatin jihar Kano ta yi na samar musu da sabon jirgin ruwa.

Ko da yake, gwamnatin jihar Kano ta bada wani tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa, wanda  ya kasance abun a Yaba, sai dai har yanzu mazauna kauyen ba su farfaɗo ba daga matsalar harkokin sufuri ba

Wakilinmu Kamaluddeen Muhammad, ya yi nazari a cikin rahotonmu na musamman na wannan mako, inda ya yi duba kan rayuwar mutanen yanking  bayan aukuwar hatsarin na ruwan Bagwai da kuma matsayar gwamnatin jihar Kano kan rashin cika alkawari ga al’ummar Badau.

Ga Cigaban Rahoton na sa.

Latsa nan domin jin cikakken rahoton.

More from Labarai