On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Har Yanzu Hukumar Kwallon Kafa Ta Kasa Bata Baiwa Kungiyar Kwallon Kafa Ta Bayelsa United Tukwicin Naira Milyan 25 Data Yi Mata Alkawari Ba

Kungiyar Kwallon kafa ta Bayelsa United

Kungiyar kwallon kafa ta Bayelsa United ta tabbatar da cewa har yanzu Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF bata bawa kungiyar Tukwicin Naira Milyan 25 da aka yi mata alkawari ba, bayan ta lashe gasar cin kofin Kalubale na kasa Aiteo na shekarar data gabata.

Shugaban sashin  yada labarai na kungiyar, Hananeel Jackson ne ya tabbatar da haka ta cikin wata sanarwa da aka fitar ranar  Talata, Yace kungiyar ta aikewa Hukumar kwallon kafa ta kasa wasikar neman basu kudaden, amma har yanzu    babu wani labari.

Kazalika ya musanta wasu rahotanni dake  cewa kungiyar  taki mayar da Kofin Gasar, Sakamakon yadda Hukumar ta NFF taki bata kudaden.

Idan ba’a manta  kungiyar ta samu nasarar  lashe kofin gasar cin Kalubale ta kasa na shekarar  2021 a karon farko bayan data doke  Nasarawa United a ranar  8 ga watan Augustan Bara.