On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Har Yanzu Ina Nan Kan Shugabancin Jam'iyyar PDP Daram, Inji Shugabanta Sanata Iyorchia Ayu

Shugaban Jam'iyyar PDP Na Kasa

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, Yace babu wani shiri da yake kan yi a halin yanzu domin yin murabus daga kan shugabancin jam’iyyar.

Da yake jawabi ta cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Simon Imobo Tsawana  ya  fitar a ranar  Litinin, Sanata Ayu , Yace  sashi  na 45 da 47 da kundin tsarin mulkin jam’iyyar  PDP yayi  bayani  dalla-dallla  kan matakan da ake bin wajen saukewa  ko kuma yin murabus daga  kan  shugabancin  jam’iyyar  PDP na kasa.

Kazalika ya kara da cewa  wasu daga cikin labarai da aka  kirkira  dake baiyana cewa ya mika  takardar murabus daga kan shugabancin jam’iyyar, ga tsohon  shugaban Majalisar dattawa David Mark, Labarai ne kawai na kanzon kurege, inda ya bukaci al’umma da yi watsi dashi.

Shugaban jam’iyyar PDPn na kasa ya kara da cewa, Da yayi murabus  to da zai mika takardar saukarsa  daga kan kujerar ne ga mataimakinsa mai kula da shiyyar Arewa ta tsakiya, ba tsohon shugaban majalisar dattawa ba.