On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Za'a Harba Bindigogi 96 Domin Girmama Marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth Ta Biyu

Marigayiya Sarauniya Elizebeth ta Biyu.

Iyalan masarautar kasar Ingila za su yi zaman makoki na kwanaki 7, wanda zai kare bayan binne sarauniya Elizabeth, tare da kuma yin kasa-kasa da tutocin dake gidan sarautar.

A  yaune Fadar mulki ta Buckingham  ta bayyana cewa,  za'a  harba bindiga da misalin karfe 1 na rana a  filin Hyde Park, inda za'a harba  bindigogi 96 wanda ya kama daidai da  adadin shekarun data yi a duiya

Masarautar dai bata sanar da lokacin binne gawar ba, sai dai ana tsinkayen  nan da kwanaki 11 za a yi mata janaza.

Queen Elizabeth new

Marigayiya Elizebeth ta Biyu, ta rasu tana da shekaru 96 a duniya.

Fadar tace za'a sauke  tutoci  zuwa kasa-kasa  a gidan sarautar kasar, har zuwa  bayan janazar tata, kana kuma zuwa lokacin makoki fadar zata kasance a rufe.