On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Har Yanzu Nine 'Dan Takarar Gwamna Na Jam'iyyar ADP A Jihar Kano - Nasiru Koguna

'Dan  takarar  gwamna  a jam’iyyar  ADP Nasiru  Koguna  yace  har  yanzun  shine  dan  takarar  gwamna  karkashin  jam’iyyar  a Kano ba  Sha’aban  sharaba  ba.

 

Cikin  wata  wasika  daya  aikewa  Hukumar  zabe  mai  zaman  kanta  ta  kasa INEC, Koguna  ta  bakin  Lauyansa  Farfesa  Nasiru  Aliyu  yace  wakilan  jam’iyya  ne  suka  zabe shi  amatsayin  Dan  takarar  jam’iyyar ADP

Kazalika  ya kara  da  cewa  shi  da  kansa  bai  rubutawa  hukumar  zabe wasika kan  janyewarsa  ba,  kamar  yadda  dokar  zabe  ta  2022  ta  tanada .

Wasikar ta kara bayyana yadda shugaban jam’iyyar na kasa ya kirkiro da sauya sunansa ba tare da bin ka’ida ba ,kamar yadda doka ta tanada.