On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Har Yanzu Nine Dan Takarar Sanatan Yobe Ta Arewa, Inji Bashir Machina.

Bashir Machina

Dan Takarar Kujerar Sanatan Yobe Ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC, Bashir Machina, Ya baiyana cewa, akwai wani yunkuri da ake yi na kwaikwayar sa hannunsa a cikin wata wasika, da nufin cewar shine ya janye daga takarar.

A cewar kwamitin yakin neman zabensa, Wasu kusoshi a cikin jam’iyyar  wadanda suka zama bayin cin hanci  da aikata lefuka  na yunkurin murde  takarar kujerar sanata ta yankin.

Wata sanarwa da kakakin Yakin Neman Zabensa, Husaini Isah, Yace matakan da ake shirin dauka wata ‘kofa ce bawa Sanata Ahmad Lawan damar darewa kan kujerar.

Daga karshe  Bashir Machina  ya  jaddada matsayarsa na cewar ba zai janye daga takarar ba, sannan kuma duk wata wasika da aka gani mai ikirarin cewa ya janye daga takarar, ba daga wajensa ta  fito ba.