On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Har Yanzu Tinubu Na Neman Wanda Zai Zama Mataimakinsa - 2023

Gabanin zaben 2023, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ce yana ci gaba da neman abokin takararsa.

Ya bayyana haka ne a Abuja a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen bikin cika shekaru 60 na shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Tsohon Gwamnan na Legas ya kuma yabawa Shugaban Majalisar kan irin gudunmawar da ya bayar wajen cika  burinsa na siyasa.

Ya kuma yaba da alakar aiki tsakanin Femi da mataimakinsa, Hon Ahmed Wase, inda ya ce yana bukatar koyi da su.

Idan za’a iya tunawa Tinubu ya zabi Ibrahim Masari, dan siyasa daga Katsina a matsayin mataimaki na wucin gadi domin cimma wa’adi hukumar zabe ta kasa  INEC kan aikewa da sunayen ‘yan takara.