On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Hatsari Ya Ritsa Da Ayarin Motocin Gwamnan Jihar Benuwe Samuel Ortom

Wani hatsarin mota ya ritsa da ayarin motocin gwamnan jihar Benuwe Samuel Ortom a birnin tarayya Abuja.

Mai taimakawa gwamnan akan harkokin yada labarai, Terver Akase shine ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa a karshen mako.

Sanarwar ta ce ba a samu rasa rai ba sanadiyar hatsarin, kuma gwamna Ortom wanda tuni ya sauka a kasar Birtaniya lafiya, yana godiya da kiraye-kirayen waya na nuna da,uwa da kauna daga mutanen jihar Benuwe da sassan Najeriya bisa jajanta ma sa kan faruwar hatsarin..