On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hsba Zata Fara Kama Masu Lika Hotunan Batsa A Babur Din Adaidaita Sahu

IBN SINA

Hukumar Hisba ta jihar kano ta yi barazanar daukar hukunci mai tsauri akan duk wani Mai tuka babur din adaidaita sahu, wanda aka samu da lika wasu hotunan batsa a jikin babur din,Ko kuma kure sautin kida a lokacin da ake tafiya.

Babban kwamandan hukumar, Sheik  Harun ibn Sina, ya  ce  da dama daga cikin masu tuka babur din na yin shiga  ta  rashin da’a,wanda  yin hakan ya sabawa  koyarwar  addinin musulunci.

A wani taron manema Labarai da hukumar ta shirya a jiya,  Ya  ce  jami’an hukumar zasu kara saka ido kan masu aikata irin wadannan lefuka, kuma za’a hukunta  su.

Dagan an sai yayi kira  a gare su das u dena  yin wasu abubuwa  da  basu  dace ba,  wadanda  suka ci karo  da  koyarwar  addinin musulunci.