On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Hukumar Bogi: Tinubu Ya Umarci ICPC Ta Gudanar da Binciken Gaggawa

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) da ta gudanar da cikakken bincike kan hukumar nan bawa shugaban kasa shawara kan al'amuran kasashen waje (PFIPC), wadda ake zargin ta bogi ce kuma tana amfani da sunan Fadar Shugaban Ƙasa ba tare da sahalewa ba.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ƙasar ya umarci ICPC ta kammala binciken tare da miƙa masa cikakken rahoto cikin kwanaki 30.

Sanarwar ta ce umarnin ya biyo bayan gano cewa PFIPC ba wata hukuma ba ce da Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kafa, kuma ba ta da wata doka, umarnin shugaban ƙasa, ko wata sahihiyar amincewar gwamnati da ta ba ta izinin wanzuwa.

An bayyana cewa wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya riƙa gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na PFIPC, tare da yin ƙaryar cewa shugaban ƙasa ne ya naɗa shi.

Shugaba Tinubu ya umarci ICPC ta binciki zarge-zargen ƙirƙirar takardun naɗi na bogi da wasu takardun gwamnati, amfani da sunan shugaban ƙasa wajen neman amincewar hukumomi da goyon bayan diflomasiyya, ciki har da sauƙaƙa samun biza, da kuma buɗe asusun bankuna da sunayen hukumomin gwamnati ta hanyar amfani da takardun da ake zargin na jabu ne.

Haka kuma, shugaban ƙasar ya umarci hukumar ta binciki ba wai mutumin da ake zargi kaɗai ba, har da duk wani wanda ya taimaka masa, tare da gano yadda wata ƙungiyar bogi da iƙirarin naɗin shugaban ƙasa suka samu karɓuwa a matsayin abin da ya yi kama da sahihiyar hukuma.

Binciken zai kuma mayar da hankali kan asalin takardun bogin da yadda aka yi amfani da su, hanyoyin da aka bi wajen neman ko samun amincewar hukumomi da goyon bayan diflomasiyya, buɗewa da gudanar da asusun bankuna masu alaƙa da lamarin, tushen kuɗaɗen da aka samu da yadda aka sarrafa su, da kuma rawar da duk wani jami'in gwamnati, mutum mai zaman kansa, banki ko wata hukuma ta taka wajen sauƙaƙa ko taimakawa wannan zargin.

Shugaban ƙasar ya kuma umarci ICPC ta gano duk wata kafa ko gibin da ke cikin tsarin gwamnati da cibiyoyinta da aka yi amfani da shi wajen aikata wannan zargi, tare da bayar da shawarwari kan matakan gaggawa da za su hana irin wannan abu sake faruwa.

Haka nan, shugaban ƙasar ya umarci dukkan ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya da su bai wa ICPC duk bayanai, takardu da goyon bayan da take buƙata bisa doka domin kammala binciken cikin gaggawa.

Tinubu ya jaddada cewa dole ne a kare mutuncin Fadar Shugaban Ƙasa da cibiyoyin gwamnatin tarayya daga masu yin sojan gona, jabun takardu, amfani da sunan gwamnati ba bisa ƙa'ida ba da kuma cin gajiyar gibin da ke cikin aikin gwamnati.

Ya kuma umarci cewa duk wanda bincike ya tabbatar da laifinsa a hukunta shi bisa tanadin doka.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 35°C | Low: 24°C