On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hukumar DSS A Najeriya Ta Musanta Janye Shari'ar Tukur Mamu

Biyo bayan rahotanni na jita-jita da ke cewa ta janye karar da aka shigar gaban kotu kan tsohon mai sasantawa da ‘yan ta’adda, Tukur Mamu, hukumar tsaro ta DSS ta musanta janye karar.

An samu rahotannin cewa hukumar ta janye karar da ta shigar gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, domin ci gaba da tsare shi na tsawon kwanaki 60 bayan kama shi.

Rahoton yace lauyan DSS, A. M. Danlami, ya shaidawa mai shari’a Nkeonye Maha matakin hukumar na janye karar.

Sai dai a wata tattaunawa da jaridar daily trust ta yi a daren ranar Alhamis, kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya, ya bayyana rahoton a matsayin na karya.

Afunanya ya ci gaba da cewa hukumar DSS ba ta taba janye karar da ake yiwa Mamu ba, yana mai cewa al’amarin na ci gaba da tafiya.