On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Hukumar DSS Ta Gargadi Yan Najeriya Masu Yin Kalaman Batanci Akan Tukur Mamu

JAMI'AN TSARO NA DSS

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta yi gargadi kan yi wadansu kalamai da basu da tushe akan kamun da ta yiwa mai sasantawa da ‘yan bindigar da suka sace fasinjojin jirgin kasa a Kaduna, Malam Tukur Mamu.

Kakakin hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya,  shine  ya bayyana haka a Abuja, inda ya ce gargadin ya zama wajibi  biyo bayan kalaman batanci da wasu jama’a suka yi kan batutuwan da suka shafi kamun da aka yiwa Tukur  Mamu da kuma bincikensa da Hukumar ke yi.

Ya ce hukumar na fatan a kyale ta ta gudanar da binciken da take yi cikin tsanaki  , wanda binciken shine  zai faiyace inda aka dosa.

Idan ba’a manta ba, jami’an yansandan kasa da kasa sun  kama Tukur  Mamu ranar Talata a birnin Alkahira na kasar Masar  yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya.

Kazalika a ranar Larabar da ta gabata ne aka dawo dashi  Najeriya inda kuma aka damka shi  hannun jami’an  hukumar  tsaro ta farin kaya DSS.