On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Hukumar EFCC Ta Kama Wasu Ma'aurata Da Ake Zargi Da Yin Damfara Ta Milyan 410

EFCC

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta gurfanar da wata mata mai suna Ai’sha Salihu Malkohi da kuma mai gidanta mai suna Abubakar Mahmoud, wanda a yanzu haka cika wandosa da iska, a gaban mai shari’a Aisha Mahmud ta babbar kotun jihar Kano, Bisa zarginsu da damfarar wata mata mai suna Farida Ibrahim tsabar kudi naira milyan 410 da dubu 518.

Hukumar ta baiyana haka ne a shafinta na X wanda aka fi sani d twitter.

Sanarwar ta ce an kama  Matar ne  biyo bayan korafin da wasu mutane biyu  Farida Ibrahim da Ibrahim Mohammed Abdulrahman  suka shigar gabanta, bisa zargin ma’auratan da  yaudararsu, da sunan  cewar  zasu kawo masu motoci da  wasu kayayyaki daga kasar Saudiyya.

To sai dai kuma matar ta musanta  tuhumar da aka karanta mata, wanda  hakan ya sa alkaliya  ta dage  zaman zuwa ranar  15 ga watan da muke ciki, domin sauraren bukatar bada ita beli.