On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hukumar EFCC Zata Yi Gwanjon Motoci 649 Data Kwace

ABDULRASHID BAWA SHUGABAN HUKUMAR EFCC

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta ce a ranar Talata mai zuwa 6 ga watan Disambar da muke ciki ne , za ta fara aikin tantancewa tare da yin gwanjon motoci 649 da aka kwace a wasu jihohi tara na kasar nan cikinsu hadda babban birnin tarayya Abuja.

Aikin da amintattun masu  gwanjon kayyakin hukumar  za su yi, zai kunshi gwanjon jiragen ruwa guda 15 da hukumar ta kama a  jihohin Rivers da Delta da kuma  Legas sai wasu  wayoyin hannu 39, Da na’urar  tafi-da-gidanka 11 da sauran kayayyaki.

A sanarwar da ta fitar a jaridar The PUNCH a ranar Juma’a, ta yi cikakken bayani kan kayayyakin da za a yi gwanjon su  kowace jiha, da ranakun da wuraren da za a yi gwanjon da shafukan internet da jama’a zasu iya amfani dasu domin kallon yadda gwanjon kayayyakin zai kasance.