On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hukumar ICPC Ta Karbo Kadarori Na Kimanin Naira Bilyan 2 Cikin Shekaru 8

TAMBARIN HUKUMAR ICPC

Hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa ta kasa ICPC, ta ce ta samu nasarar karbo kadarori na kimanin Naira biliyan 2 da milyan Dari 8 a cikin shekaru uku da suka gabata ta karkashin shirin ta na bin diddigin ayyukan mazabu da kuma wanda bangaren zartarwa ke gudanarwa.

Kwamishinan Hukumar ICPC a jihar Edo, Mista Agwu Amefula, Shi ne  ya bayyana haka a ranar Talata a Benin babban birnin jihar,  yayin da yake  jawabi a wajen wani  taron wayar da kan jama’a da masu fada a ji na jihar da hukumar ta shirya.

Ya kara da cewa,  hukumar ta tilastawa   ‘yan kwangila  450 komawa   wuraren aiyukan da aka yi  watsi da su koma babu aikin domin kammala su.

Sai dai ya bukaci masu ruwa da tsaki da su sanya ido sosai kan abubuwan da suka shafi  cin hanci da karbar  rashawa da kuma tabbatar da gaskiya da adalci , wanda a cewarsa matsaloli ne da suka yi kaurin suna ta bangaren  gudanar da aiyukan gwamnati a cikin al’umma.