On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Hukumar Kidaya Ta kashe Bilyan 200 Kan Aikin Kidaya

Nasir Kwarra

Hukumar Kidaya ta kasa ta ce ta kashe jimillar kudi har naira milyan dubu 200 domin kimtsawa aikin kidayar mutane da gidaje ta shekarar bana, kamar yadda shugaban hukumar Nasir Kwarra ya baiyyana.

Ya  fadawa manema labarai  cewar kudin da aka kashe wani bangare ne  na naira bilyan 800  da ake  saran  karba daga  hannun gwamnatin taraiyya, a matsayin kasafin da  ta yi domin gudanar da aikin kidayar.

Ya  ce kudin an kashe su ne  bayan shafe  kusan shekara  biyar  ana  tsara  yadda za’agudanar da aikin kidayar.

Ya  kuma  baiyana cewar  gudanar da aikin kidayar  a zamanance  abu ne mai girman gaske,  kasancewar  dole ne  hukumar  sai ta  sayi  Data wadda  za’a yi amfani da ita wajen gudanar da aikin.