On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Hukumar Kiyaye Afkuwar Haddura A Najeriya Na Shirin Farautar Manyan Motoci Masu Dakon Dabbobi Hade Da Mutane

Hukumar kiyaye hadurra ta tarayya ta tabbatar da mutuwar mutane 18 a wani hadarin mota da ya afku a hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar Lahadi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Bisi Kazeem ya sanya wa hannu, ta ce hatsarin ya afku ne da karfe 05:20 na Asuba a kauyen Audu Jhangon da tireloli dauke da mutane da dabbobi wadanda da alama matafiyan dare ne.

Ya ce hatsarin ya rutsa da mutane 65 daga cikinsu,  mutane 27 da suka samu raunuka daban-daban an kai su asibiti mafi kusa domin yi musu magani.

Ya kara da cewa, biyo bayan afkuwar al’amarin, shugaban hukumar, Dauda Biu, ya kafa wata rundunar hadin gwiwa da za ta gudanar da aikin sintiri na musamman domin  kamo tireloli da manyan motoci dauke da mutane hade da dabbobi.