On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hukumar Kwastam Ta Kama Wani Buhu Makare Da Kakin Soja

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta kasa reshen jihar Kaduna, Ta samu nasarar cafke wani Buhu Makare da Kakin soja wanda ake kan hanyar shigo dashi kasar nan daga Jamhuriyar Nijar, Daga tsakanin watan Maris zuwa Aprilun bana.

Shugaban hukumar  reshen  Kaduna, Musa Jalo  wanda  ya tabbatar da haka ta cikin wata sanarwa  da  ya fitar  a ranar Alhamis , Ya  ce jami’ansu sun kama wata mota  kirar Golf  Volkswagen da wani  dan Najeriya ke tuka  ta  akan  hanyar  Jibia zuwa katsina.

Ya kara da cewar, Jami’ansu  sun  ga  buhun dake cikin motar, wanda  nan take suka bude  shi,inda suka yi arba  da kakin soji,  wanda  ya  hada  da  kananan riguna da wanduna  da  sauransu.

Ya  ce  bincikensu ya gano cewar  direban motar  Dan asalin Najeriya ne, Kuma  yana kan hanyar  kai kayan ne  zuwa wajen wani mutum a jihar Katsina.

Ya kara  da cewar tuni aka  mika buhun kayan  ga hannun hukumar  tsaro ta farin kaya domin  zurfafa  bincike, da kuma gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu.