On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Hukumar NAFDAC Ta Ja Hankalin Jama'a Kan Amfani Da Wani Maganin Tari Mai Kisan Farat Daya

NAFDAC

Hukumar kula da ingancin Abinci da Magunguna ta kasa NAFDAC ta ja hankalin ‘yan Najeriya kan yin amfani da wani maganin Tari mai suna NATUR COLD.

Shugabar  hukumar  farfesa  Mojisola Adeyeye  ta  baiyana cewar  maganin tarin ya yi sanadin mutuwar kananan yara  har  guda shida a kasar Kamaru.

Ta baiyana  cewar maganin tarin na NATUR COLD  baya  cikin magungunan data amince  dasu,  sannan kuma ta  ja  kunnen  masu rarraba  maganin  da kuma samar dashi  da su kuka da kansu.

Kazalika  ta yi kira  ga masu shigo da maganin da  siyar  da  shi  ga  jama’a dasu gaggauta denawa.