On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Hukumar Sufurin Jiragen Sama Na Bincike Kan Batan Hanyar Da Jirgin United Air Ya Yi

Hukumar kula da sufurin jirage sama ta kasa ta fara bincike kan dalilan da suka sa wani jirgin United Nigeriya Samfurin NUA 0506 da ya kamata ya sauka birnin Taraiyya Abuja, amma ya yi batan hanya inda ya sauka birnin Asaba na jihar Delta.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da  shugaban hukumar Kaftin Musa Nuhu ya fitar a ranar Litinin a Abuja.

Lamarin dai  ya haifar da cece kuce a tsakanin  jama’a musamman a kafafen sadarwar zamani.

Sai dai Hukumar  ta  baiwa jama’a tabbacin cewar  zata yi bincike  na tsanaki  sannan kuma ta   sake jaddada  kare  lafiyar  masu amfani da jiragen sama a kasar nan.