On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Hukumar Zabe Ta Bukaci Kotu Ta Hana Yin Amfani Da Katin Zabe Na Wucin Gadi

SHUGABAN HUKUMAR ZABE TA KASA

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta bukaci Kotun daukaka kara dake zamanta a Abuja, Data jingine hukuncin da wata babbar kotun taraiyya ta yi, inda ta umarci hukumar zaben ta kasa data baiwa wadansu mutane biyu damar yin amfani da katin zabensu na wucin gadi domin yin zabe.

A kunshin  karar  da hukumar  zaben ta shigar  gaban kotun,   Hukumar ta nemi  kotun  daukaka  karar  data  dakatar da zartar  da hukuncin da babbar  kotun taraiyyar  ta yi a ranar   9 ga watan Maris  din bana,har sai  zuwa lokacin da zata  kammala  sauraren karar  data  shigar  gabanta.

Kazalika  hukumar  zaben  ta kasa  taga baiken  hukuncin da   babbar  kotun taraiyyar  ta yanke,  wanda  ta aiyana cewar  babu  inda  aka yi  magana  kan  batun katin zabe  a cikin dokar zabe  ta shekarar  2022,  wanda  ta kafa  hujja  da hakan  a matsayin abunda  zai bada damar yin zabe.

Idan ba’a manta  ba, mutanen da suka kai karar  hukumar zabe  ta kasa  a babbar kotun data  yanke  hukunci  tun  da  farko,sun baiyana cewar  duk da kokarin da  suka rika yi  na ganin  sun karbi  katinan zabensu na din-din din,hakan bai yuwu ba.