On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Hukumar Zabe Ta Kasa Zata Horas Da Ma'aikata Sama Da Milyan Daya Da Zasu Yi Aikin Zabe

ZABE

Hukumar zabe ta kasa Mai zaman kanta ta ce zata horar da ma'aikatan wucin gadi da miliyan 1 da dubu Dari hudu da zasuyi aikin zaben shekarar 2023.

Daraktan cibiyar bada horo kan harkokin zabe ta hukumar,Sa'ad Idris shine ya bayyana haka a ranar talata a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a wani  taron karawa juna da aka shirya a birnin Ikko.

Yace daga cikin ma'aikatan da  za a horas sun hada da jamian sa ido da jamian tattara bayanai da dai sauran su.

Kazalika ya kara da cewa hukumar zata samar da kayan aiki domin tabbatar da cewa anyi sahihin zabe a kasar nan.