On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Hukumar Zabe Ta Zargi Yan Siyasa Da Siyen Katinan Zabe Na Din-din-din

KATINAN ZABE

Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta ta zargi wasu ‘yan siyasa da siyan katinan zabe na din-dindin domin yin amfani da lambobinsu gabanin babban zabe na shekarar 2023.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da  kwamishinan hukumar mai kula da birnin tarayya Abuja da  jihohin  Nasarawa da kaduna da kuma Filato mohammed Haruna.

Ya ce kwanan nan an yanke wa wasu mutane biyu hukunci, bisa laifin mallakar katinan zabe  ba bisa ka’ida ba a jihohin sokoto da kano.

Kalaman da hukumar ta INEC tayi,  ya janyo cece-ku-ce daga wasu masu ruwa da tsaki, wadanda suka hada da Kungiyar  afenifere, data Pandef sai kungiyar ohanaeze ndigbo da  sauransu.