On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Hukumar Zabe Tace Kwanaki Tara Ya Rage A Dakatar Da Rijistar katin Zabe Na Din-din-din

KATIN ZABE

Hukumar Zabe Ta kasa Mai zaman Kanta INEC, Ta sake fadakar da Yan Najeriya cewa , Hukumar zata dakatar da aikin rijistar katin zabe na din-din da ake kan yin a da kwanaki Tara masu zuwa .

Wani jami’in hukumar, Luka Buba ne ya baiyana  haka, kazalika  shima babban  jami’in  kula da rijistar katin zabe na Hukumar, Temi, Ya baiyana cewa Hukumar zata soke duk wata rijistar katin zabe data samu anyi ta har sau biyu.

Kazalika yace za’a iya magance matsalolin da suka danganci bacewar katin zabe akan shafin hukumar zabe na Internet.

A wani bangaren kuma,Hukumar  Zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, Tace a yaune zata wallafa sunayen yan takarar da jam’iyyu suka  gabatar mata, a matsayin yan takararsu na  gwamna da  Yan Majalisun Dokokin Jihohi  na fadin kasar nan.

Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood  Yakubu ne ya baiyana haka a lokacin da yake rantsar da sabon kwamishinan zabe na birnin taraiyya Abuja.

Sai dai kuma, Shugaban Hukumar ya baiyana damuwarsa  game da karuwar  rikicin cikin gida a tsakanin jam’iyyu, wanda shine ya zama babban  tarnaki ga tsarin gudanar da zabe a kasar nan.

Ya kara da cewa, hukumar zata cigaba da hada kai da jam’iyyu domin wayar masu da kai dan ganin sun kasance masu bin doka da oda.