On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

HukumarZabe Ta Ce Karancin Kudi A Hannu Zai Iya Kawo Tazgaro Wajen Gudanar Da Zabe Mai Zuwa

shugaban hukumar zabe farfesa Mahmood Yakubu

Yayin da ya rage kwanaki goma sha shida a fara gudanar da babban zaben kasar nan, akwai wasu rahotanni dake baiyana cewa karancin sabbin kudin da aka sauyawa fasali ka iya kawo tazagaro wajen gudanar da zaben mai zuwa.

Shugaban hukumar  zabe   ta kasa,  Farfesa  Mahmood  Yakubu  ne  ya  baiyana haka a  yayin ganawarsa  da  gwamnan  babban  bankin kasa, Godwin Emefiele  a  shalkwatar  bankin  dake  Abuja a ranar  Talata.

Ya  kara  da  cewa  mafi  yawa  daga  cikin   wadanda  zasu   gudanarwa  da  hukumar  wasu  aikace  aikace a  lokacin  zaben  basu  da  asusun  banki.

A  saboda  haka  shugaban  hukumar zaben  ta kasa,Ya yi  kira  ga Babban bankin kasa  da  ya gaggauta  magance  matsalar da   shirin  takaita  zagayawar  kudi  a hannun  jama’a  ta  haifar  a  fadin kasa   a  yanzu  haka.