On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

ICPC Ta Kama Likitan El-Rufai Kan Zargin Take Umarnin Kotu

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ta sanar da kama Farfesa Bello Abubakar, likitan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, bisa zargin bayar da bayanan ƙarya bayan wata ziyarar duba lafiya da kotu ta amince a yi wa tsohon gwamnan yayin da yake tsare a hannun hukumar.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, J. Okor Odey, ya fitar a ranar Talata, ICPC ta zargi El-Rufai da likitansa da karya sharuddan umarnin kotu da ya ba shi damar zuwa asibiti domin duba lafiyar sa.

Hukumar ta ce Babbar Kotun Jihar Kaduna ta ware ranakun 6, 7 da 8 ga watan Yulin 2026 domin ci gaba da sauraron shari'ar da ake yi wa El-Rufai cikin gaggawa, amma bai gurfana a gaban kotun ba a ranar farko na zaman.

A cewar ICPC, masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotun cewa lokacin da jami'an hukumar suka shirya kai El-Rufai kotu, ya ƙi tafiya, yana mai cewa yana son ganin likitansa na kashin kansa.

Hukumar ta ce ba a gabatar mata da wata buƙata kafin wannan ziyarar duba lafiya ba, sannan ta yi iƙirarin cewa lokacin da likitan hukumar ya tambaye shi, El-Rufai ya ce ba shi da wata matsalar lafiya ta gaggawa, sai dai matarsa, Asia El-Rufai, wadda kuma na cikin lauyoyinsa, ce ta buƙaci ya ga likitansa, Farfesa Bello Abubakar.

Bayan sauraron hujjojin ɓangarorin biyu, kotun ta ɗage shari'ar zuwa ranar 15 ga Yulin 2026 domin sauraron buƙatar da El-Rufai ya gabatar na janyewar alkalin da ke sauraron shari'ar, tare da jiran umarnin Babban Alƙalin Jihar Kaduna kan buƙatar sauya wurin sauraron shari'ar.

ICPC ta ce duk da haka, ta bi umarnin kotu tare da ba El-Rufai damar zuwa sashen masu zaman kansu na Asibitin Ƙasa da ke Abuja domin duba lafiyarsa, ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro.

Hukumar ta bayyana cewa jami'anta na lafiya da tsaro sun tsaya a wajen ɗakin da ake duba lafiyar El-Rufai bisa buƙatar 'yan uwansa, domin ba likitan da ke kula da shi damar gudanar da aikinsa cikin sirri.

Sai dai ICPC ta ce daga baya ta ga wasu hotuna da ɗaya daga cikin abokan siyasar El-Rufai, Isa Ashiru Kudan, ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya bayyana cewa sun kammala ganawa da tsohon gwamnan a lokacin da ake tsammanin cewa ana duba lafiyar ta sa.

A cewar hukumar, hotunan sun nuna Isa Ashiru Kudan, Farfesa Bello Abubakar da wasu mutum uku tare da El-Rufai, lamarin da ta ce ya nuna an yi amfani da damar zuwa asibitin wajen wasu ayyuka da ba sa cikin abin da kotu da ICPC suka amince da shi.

Hukumar ta bayyana hakan a matsayin take umarnin kotu, tare da cewa za ta gabatar da lamarin a gaban kotu domin ɗaukar matakin da ya dace.

ICPC ta ƙara da cewa ta kasance mai haƙuri, ƙwarewa da mutunta haƙƙin dukkan waɗanda ke tsare a hannunta, amma ba za ta ci gaba da lamuntar cin zarafin wannan karamci ba.

Hukumar ta kuma sanar da cewa ta kama Farfesa Bello Abubakar domin cigaba da bincike kan zargin bayar da bayanan ƙarya, tare da jaddada cewa za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta bisa tanadin doka, kuma ba za ta amince da duk wani yunƙuri na cin moriyar kyakkyawar niyyarta ba.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 35°C | Low: 24°C