On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

INEC Na Gab Da Yin Baje Kolin Masu Rijistar Katin Zabe A Najeriya

SHUGABAN HUKUMAR ZABE TA KASA

Hukumar Zabe ta kasa mai zaman kanta, tace tana kan aikin wallafa cikakkun bayanaan yawan ‘yan Najeriyar da suka yi rijistar katin zabe, gabanin babban zaben shekarar 2023 dake tafe.

Shugaban hukumar, farfesa Mahmood Yakubu ne ya baiyana haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki, domin yin nazari kan kundin dokoki da  tsare-tsaren kada kuri’a  ga ‘yan gudun hijira da aka yiwa gyaran fuska, yau a Abuja.

Yace sunayen, zai kunshi sabbin wadanda suka yi rijistar katin zabe, kari akan milyan 84 da ake  dasu.

Bugu da kari, Shugaban Hukumar Zabe ta kasa, yaga baiken wasu kungiyoyin farar hula dake baiyana cewa, Hukumar zaben ta kasa bata da niyyar baje kolin wadanda suka yi rijistar katin zabe, inda hukumar ta baiyana cewa tayi baje kolin rijistar katin zaben  har sau ukku, wand aya hada da ranar 24  da 30  ga  watan  Satumbar 2021, da kuma 24 ga watan Disambar 2021.