On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

INEC ta Dage Wa'adin Gabatar da Sunayen 'Yan Takara

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsawaita wa’adin da ta bai wa jam’iyyun siyasa na gabatar da sunayen ‘yan takarkarin su na zaben 2027 da karin kwanaki uku.

Hukumar ta sanar da cewa wa’adin, wanda tun farko zai kare a ranar Asabar, 11 ga Yulin 2026, yanzu an tsawaita shi zuwa tsakar daren ranar Talata, 14 ga Yulin 2026.

Hukumar ta INEC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, wadda Kwamishinan Hukumar kuma Shugaban Kwamitin Wayar da Kan Masu Kada Kuri’a da Ilimantar da su, Mohammed Kudu Haruna, ya sanya wa hannu.

A cewar hukumar, an tsawaita wa’adin ne bayan bukatar da Majalisar kula da kuma bada shawarwari tsakanin Jam’iyyun Siyasa (IPAC) ta gabatar a madadin jam’iyyun siyasa da ba su samu damar loda sunayen ‘yan takararsu ba cikin wa’adin da aka gindaya ba.

Sanarwar ta ce, “An yanke shawarar tsawaita wa’adin ne bisa rokon da IPAC ta gabatar a madadin jam’iyyun siyasa da ba su kammala saka sunayen ‘yan takararsu da bayanansu cikin lokacin da aka tsara ba.”

INEC ta ce tsawaita wa’adin na nuna kudurinta na tabbatar da kowa ya samu damar shiga tsarin zabe, tare da bin tanade-tanaden doka.

Hukumar ta kuma bukaci dukkan jam’iyyun siyasa da su yi amfani da karin lokacin domin kammala gabatar da bayanan ‘yan takararsu kafin cikar sabon wa’adin.

Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar na kira ga jam’iyyun siyasa da su yi amfani da wannan dama wajen tabbatar da cewa sun loda dukkan bayanan da ake bukata kafin sabon wa’adin ya cika.”

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 35°C | Low: 23°C