On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

INEC Ta Mika Shaidar Nasarar Zaben Gwamnan Kano Na 2023 Ga Abba Kabir

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta gabatar da shaidar Nasarar zaben 2023 ga zababben gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar NNPP Injiniya Abba Kabir Yusuf.

Abba ya karbi shaidar a shalkwatar hukumar zabe INEC reshen Jihar Kano yayinda ake gabatar da shaidar da sauran zababbun 'yan Majalissar dokokin Jihar Kano karkashin jam'iyyun APC da NNPP.

Ana gabatar da irin wannan tajardar shaidar cin zabe a sauran jahohin Najeriya 28 da aka gudanar da zaben gwamna da 'yan Majalissar dokokin Jiha ranar 18 ga watan Maris 2023.

A Kano tunda farko Abba Kabir ya gayyaci al’ummar jihar zuwa hukumar Zabe reshen Kano, domin su shaida miƙa masa takardar lashe zaben Gwamnan Kano tare da mataimakinsa, Kwamred Abdulsalam Gwarzo a ranar  laraba.

A cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ga manema labarai a ranar Talata, ya yi fatan mahalarta taron zasu kiyaye bin dokoki.