An sake rufe mashigar ruwa ta Hormuz, wacce ke zama muhimmiyar hanyar jigilar danyen mai da kayayyakin man fetur zuwa Turai, Asiya da sauran sassan duniya, sakamakon sabon rikicin da ya barke tsakanin Amurka da Iran.
Tun farko an rufe mashigin ne a lokacin yakin da ya hada Amurka da Isra'ila da Iran, lamarin da ya haddasa tashin farashin man fetur a sassa daban-daban na duniya.
Bayan kimanin watanni shida, Amurka da Iran sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya, wanda ya sa aka sake bude mashigar. Sai dai a cikin 'yan kwanakin nan dangantaka tsakanin kasashen biyu ta sake tsami, inda Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar ta rushe.
Da safiyar Lahadi, rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da rufe mashigar Hormuz na wani lokaci ba tare da kayyade ranar budewa ba.
Hakan kuwa na zuwa ne bayan harbin gargadi da Iran ta yiwa wani jirgin ruwa da ta ce ya yi kokarin wucewa ta wata hanyar da ba a amince da ita ba.
A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya wallafa, rundunar ta zargi kasashen waje da katsalandan tare da bayyana cewa ba za a bari wani jirgin ruwa ko na yaki ya ratsa mashigar ba har sai an dakatar da abin da ta kira tsoma bakin Amurka a yankin.
A nata bangaren, rundunar sojin Amurka ta ce ta kaddamar da sabon hari kan Iran bayan dakarun IRGC sun kai hari kan wani jirgin dakon kaya mai tutar Cyprus da ke wucewa ta mashigin, inda aka ce har yanzu ana neman daya daga cikin ma'aikatan jirgin.
Comments
Add a comment