On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Iyayen Daliban Oriire sun Bayyana Shakku Kan Komawar Yayan su Makaranta

Wasu iyaye da 'yan uwan daliban da aka kubutar bayan shafe kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane sun bayyana cewa har yanzu ba su da niyyar mayar da 'ya'yansu makarantun da aka sace su a Karamar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo.

Iyalan sun bayyana hakan ne bayan kubutar da daliban da malamansu daga hannun masu garkuwa, inda suka ce duk da farin cikin dawowarsu gida, har yanzu firgicin abin da ya faru na damunsu.

Sun gode wa Allah da gwamnatin tarayya da jami'an tsaro da duk wadanda suka taka rawa wajen kubutar da yaran, amma suka ce abin da suka fuskanta ya bar musu rauni da ba zai sa su gaggauta mayar da su makarantun da abin ya faru ba.

A cewarsu, yaran sun shafe kwanaki 56 a cikin dazukan da ke kusa da Old Oyo National Park bayan da masu garkuwa suka kai hari kan makarantunsu. Sun kuma ce malamai biyu sun rasa rayukansu yayin harin, kafin jami'an tsaro su kubutar da sauran wadanda aka sace.

Wasu daga cikin iyayen sun ce suna duba yiwuwar sauya wa 'ya'yansu makaranta saboda tsoron kada irin wannan lamari ya sake faruwa.

Sun jaddada cewa dole ne gwamnati ta tabbatar da ingantaccen tsaro a makarantu kafin su amince yaran su koma karatu a wuraren da aka sace su.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thunder storm

    High: 33°C | Low: 23°C