On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Iyayen Yara Sun Bukaci Tinubu Ya Hana Kara Kudin Makaranta

Kungiyar iyayen yara ta kasa ta roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da hana ma’aikatar ilimi ta kasa yin karin kudin makaranta da kaso 100 bisa 100, da Daliban kwalejojin gwamnati da kuma na Makarantun Hadaka ke biya a kasar nan.

Kungiyar  ta baiyana karin a matsayin kuntatawa, sannan kuma bai dace da lokacin da ake  ciki ba,  wanda  kuma ya  ci karo da alkawarin da  shugaban kasa  Tinubu  ya yi,na kyautata rayuwar iyayen yara, sakamakon kalubalen  cire  tallafin mai.

A wata sanarwa da babban jami’in kungiyar na kasa, Monday Eze  ya fitar, Ya koka kan karancin gogaggun malamai da dakunan kwana da Ajujuwa da  kuma rashin bada horo kan darussan kimiyya da fasaha a kwalejojin kimiyya da fasaha  guda  shida da ake dasu a shiyyoyin kasar nan.

Ya  bukaci sabuwar  gwamnati data samar da muhimman kayayyakin a  makarantun domin ingantasu.