On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

JAMB Zata Hukunta Masu Cibiyoyin Na'ura Mai Kwakwalwa Dake Karbar Sama Da Naira 700 Daga Hannun Masu Rubuta Jarabawar ta

JAMB

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu Ta Kasa JAMB, Ta ja kunnen Masu cibiyoyin Na’ura Mai Kwakwalwa da ake rubuta jarabawar, Da su guji karbar kudi daga hannun masu rubuta jarabawar ko kuma su fuskanci Hukunci mai tsauri.

A mujallarta ta Mako-Mako da take wallafawa, Hukumar  tace an jawo hankalinta game da yadda wasu masu wuraren cibiyoyin rubuta jarabawar, ke karbar sama da naira 700   daga hannun Masu rubuta jarabawar, da sunan biyan kudin aikin da suka yi masu.

Hukumar tace ba zata saurarawa duk wanda aka samu da aikata lefin karbar kudi  ba, sannan kuma zata ci tarar naira dubu 100 aka duk wanda aka samu da aikata wannan lefi.

Daga  nan Hukumar JAMB ta shawarci masu rubuta jarabawar ta da su kai rahoton  duk wata cibiyar na’ura mai Kwakwalwa  da aka samu tana karbar kudi fiye da naira 700  da sunan kudin aiki.