On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Wata Maboyar Masu Garkuwa Da Mutane A Kano

Hadakar Jami’an tsaro sun kubutar da wata dattijuwa Fatima Ibrahim da wasu ‘yan bindiga sukayi garkuwa da ita a karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.

Da yake tabbatar da kubutar da dattijuwar, Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa Lawan Shisu, yace jami’an tsaron sunyi nasarara da karfe 5 asuba a ranar asabar bayan anyi garkuwa da ita a ranar larabar makon jiya a a kauyen Sangayawa da ke karamar hukumar Kiyawa  ta jihar Jigawa.

Yace an kama mutane 4 daga cikin maharan da ake zargi, sannan an gano motoci 2 a tare da su bayan tarwatsa maboyarsu a kauyen tafasa dake karamar hukumar Ajingi ta jihar Kano.

Shisu, yace an mika Hajiya Fatima ga iyalanta yayinda bincike ke cigaba da kankama.