On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Jami'ar Bayero Kano Ta Musanta Rahotannin Karin Kudin Makaranta Ga 'Dalibai - BUK

Jami’ar Bayero dake  Kano ta musanta rahotanni da ake yadawa a kafafen sada zumunta na zamani da ke bayyana karin kudin makaranta.

Wata sanarwa da mataimakin magatakardar mai kula da harkokin yada labarai, Lamara Garba ya fitar ta ce wasikar da ake yadawa  bata da tushe.

Sanarwar ta ce har yanzu mahukuntan jami’ar ba su yanke hukunci kan duk wani karin kudin makaranta ba sabanin yadda ake yadawa a shafukan sada zumunta.

Ya bukaci  dalibai da iyaye da sauran masu ruwa da tsaki su lura cewa har yanzu Jami’ar Bayero ba ta yanke shawara kan karin kudin makaranta ba.