On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jami’ar Bayero Ta Karyata Rahotannin Yin Garkuwa Da Dalibanta A Jami'ar

BUK

Jami’ar Bayero dake nan Kano, ta baiyana wasu rahotanni dake cewar an samu matsalar garkuwa da mutane ko kuma matsala ta rashin a jami’ar, a matsayin ‘karya da basu da tushe balle makama.

Wata sanarwa da mataimakin magatakardan jami’ar Bayero, Lamara Garba  ya aikowa Arewa Radiyo a daren jiya, Ta jadadda cewar  labaran na zuki ta malli ne.

Sanarwar ta  baiyana cewar jami’ar  ta yi matukar damuwa  da yadda wasu mutane marassa zuciya  zasu kirkiri  labarin bogi, wanda suka san cewar  zai haddasa  rudani a cikin jami’ar ta Bayero dama jihar Kano baki daya.

Lamara Garba y ace  jami’ar Bayero tana cikin aminci da kwanciyar hankali da zaman lafiya, a saboda haka jama’a  suyi watsi  da labarin da aka kirkira, wanda ke nuna an samu wata barazana ta rashin tsaro  a jami’ar.