On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Jami'ar Kimiyya Da Fasaha Ta Wudil Tace Ba Zata Juyawa ASUU Baya Ba

KOFAR SHIGA JAMI'AR KIMIYYA DA FASAHA TA WUDIL

Jami’ar kimiyya da fasaha dake Wudil ta bayyana cewa bata da niyyar ficewa daga yajin aikin da kungiyar jami’oi ta kasa ke cigaba da gudanarwa.

Shugaban kungiyar ASUU a jami’ar dake Wudil Mohammed Sani Gaya yayin ganawa da wakiliyar mu Mary Emmanuel, ya jaddada cewa yunkurin da gwamnatin tarayya keyi na raba kan mombobin kungiyar ba zaiyi aiki ba, don babu jami’ar da zata fice daga yajin aikin.

An dai samu rahotanni dake cewa wasu jamioin jihohi da suka hadar da jami’ar jihar Kaduna KASU da jami’ar jihar Ekiti EKSU, da jihar Nasarawa dake Keffi sun fice daga yajin aikin sai baba ta gani da uwar kungiyar ke gudanarwa.

Ya kuma  jaddada cewa jami’oin jihohi dake gudanar da harkokin koyo da koyarwa dama basa cikin kungiyar ta ASUU, yayin da kuma aka dakatar da wasu tun a baya, kuma ba zasu amfana da duk wani cigaba da kungiyar ta samo ba.

More from Labarai