On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

Jam'iyyar ADC Ta Nesanta Kanta Daga Goyon Bayan Takarar Peter Obi A Zaben 2023

Wani tsagi  na jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata. Patricia Akwashiki ya nesanta kansa daga zargin goyon bayan wasu jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu a 2023 da wani bangare na jam’iyyar ya yi.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wani bangare na jam'iyyar ADC ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi a ranar Litinin.

Shugabar jam’iyyar ADC, Sanata Patricia Akwashiki a wata sanarwa da ta fitar a Abuja, ta bayyana amincewar a matsayin ha’inci, maras amfani kuma babu wani tasiri da hakan zai yi tunda wani bangare na jam’iyyar ne ya mika kansa domin burin  samun kudi.

Ta zargi wani bangare na jam’iyyar, karkashin jagorancin Ralph Nwosu, da laifin kin jinin jam’iyyar da yi ma ta zagon kasa.

Tunda farko dai a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ciikin wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban tsagin jamiyyar ADC na kasa Raphael Nwosu, da kuma Pat Utomi tare da wani  na  hannun daman Obi.

Yayin jawabin sa shugaban na LP farfesa Pat Utomi, ya bukaci mambobin jamiyyar da su zauna lafiya domin cigaban jamiyyar da manufofin ta, ta hanyar kare kuri’un su da saita kasar nan.