On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Jam'iyyar APC A Kano Zata Dakile Inconclusive A Zaben 2023 - Muhammad Garba

Jam’iyyar APC a jihar Kano na shirin hada matasa sama da miliyan daya a fadin kananan hukumomi 44 domin hana sake faruwar zaben Incoclusive da akayi a shekarar 2019.

Mai magana da yawun tawagar  yakin neman zaben Gawuna da Garo kuma kwamishinan yada labarai Mallam Muhammad Garba  ya ce jam’iyyar APC na son ganin an kammala zaben gwamna a 2023 a zagayen farko na zaben.

Ya ce a shekarar 2019, ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP a wancan lokacin, mafi yawansu a jam’iyyar NNPP a yanzu, sun kammala magudin zabe wanda ya kai ga bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.

Idan za’a iya tunawa  zaben da ba a kammala ba a karshe gwamna Abdullahi Ganduje ya yi nasara a kan jam’iyyar PDP da ke kan gaba kafin a bayyana zaben amatsayin wanda bai kammalu ba.