On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Jam'iyyar APC Ta Bukaci A Kama Atiku Abubakar Bisa Zargin Laifukan Rashawa

Majalisar yakin neman zaben Tinubu da Shattima tayi kira da’a kama tare da gurfanar da dan takarar shugaban kasa karkashin jamiyyar PDP Atiku Abubakar a gaban kotu sakamakon zarginsa da aikata almundahanar wasu kudade da kuma karya dokar Penal code.

 

Majalisar ta bakin mai jami’an yada labaranta Dele Alake, Festus Keyamo, Bayo Onanuga da Femi Fani Kayode da kuma Idris Mohammed, sunyi  wannan kira ne a yayin ganawa da manema labarai a Abuja, suna masu cewa Atiku bashi da wata kariya.

Sun kuma bukaci Atiku daya janye daga takarar shugabancin kasa.

A cewar su, majalisar yakin neman zaben zata dauki matakin shari’a da zai dakatar da tsohon mataimakin shugaban kasar daga tsayawa takara a babban zaben dake tafe a wata mai zuwa kan zargin aikata cin hanci da rashawa.

Sai dai a wani martani,  mataimaki na musamman ga dan takarar shugabancin kasarnan a jamiyyar PDP Abdulrasheed Shehu Sharada, yace jamiyya mai mulki ta APC tare da dan takarar ta, suna kame-kamene kawai, sakamakon sun rasa kwarin gwiwar sun a lashe zaben dake karatowa.

Da yake zantawa da Arewa radio a yammacin nan, Shehu ya kara da cewa wasu daga cikin zarge zargen da suke a yanzu ba wani sabon abu bane, wanda suke yadawa da daidaikun mutane ko wasu rukuni, bisa tuhumar cin hanci da rashawa ga tsohon mataimakin shugaban kasar.

Kazalika kakakin ya nuna mamakin sa kan yadda masu magana da yawun Tinubu suke nuna yatsa kan zargin da ake yi ga dan takarrar shugabancin kasar, na jamiyyar adawar su wanda ba a tabbatar ba.